Wenger ba ya son Chile ta sa Sanchez

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bukaci Chile
kada ta yi gangancin sanya Alexis Sanchez a
wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin
duniya da za ta yi da Uruguay.
Dan wasan mai shekara 27 bai buga wasan da
Chile da Colombia suka tashi 0-0 ranar Alhamis
ba saboda raunin da ya ji.
Jami'an kula da lafiya na Chile sun sa ran zai
samu sauki kafin wasan da kasar za ta yi da
Uruguay ranar Talata a Santiago.
Wenger ya shaida wa kafar watsa labarai ta beIn
Sports cewa a kodayaushe Sanchez "Yana son
buga wasa, kuma a shirye yake ya taka leda ko
da kuwa lokacin da ya ji rauni ne."
Sanchez, wanda ya zura kwallo takwas a
wasannin da ya buga wa Arsenal a kakar wasa
ta bana, ya zaune a benchi kusan tsawon wata
biyu a kakar wasan da ta wuce saboda raunin da
ya yi.
Wenger ya kara da cewa "Batun rashin lafiyar
tasa abu ne mai muhimmanci a tsakanin
kungiyar kwallon kafar kasarsa da kuma kulob
dinsa, amma dai ya kamata mu bai wa lafiyarsa
muhimmanci."
Kocin na Arsenal ya ce za a dauki hoton wurin
da dan wasan ya ji rauni domin sanin irin
maganin da za a yi masa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wenger ba ya son Chile ta sa Sanchez"

Post a Comment