Mark Zuckerberg ya kare Facebook kan zaben Trump

Mai kamfanin sada zumunta na Facebook Mark
Zuckerberg ya kare shafin saboda zargin da aka
yi masa cewa Facebook ne ya rika watsa labaran
kanzon-kurege da suka bai wa Donald Trump
nasarar zama shugaban Amurka.
Mr Zuckerberg, wanda ya yi jawabi a wurin wani
taro kan fasaha da aka yi a California, ya ce bai
kamata a dora wa Facebook alhakin cin zaben
Trump ba.
A cewarsa, "Tunanin da wasu ke yi cewa
Facebook ya watsa labaran kanzon-kuregen da
suka yi tasiri a zaben kasar nan ba daidai ba ne."
Shugaban kamfanin na Facebook ya kara da
cewa duk wanda ya amince cewa Facebook ya yi
tasiri a zaben, bai fahimci irin sakonnin da
magoya bayan Trump ke son isar wa a lokacin
yakin neman zabe ba.
Wasu bayanai dai sun nuna cewa an rika watsa
labaran karairayi wadanda suka bai wa Trump
damar yin nasara fiye da labarai na gaskiya a
shafin Facebook.
Mutane da dama, musamman Amurkawa, sun
mayar da Facebook wani dandali da suka fi
samun labarai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mark Zuckerberg ya kare Facebook kan zaben Trump"

Post a Comment