BBC za ta bude sabbin sassan harsuna 11

BBC ta kaddamar da wani shirin fadada aikace-
aikacenta a sashenta mai watsa shirye-shirye
zuwa kasashen waje mafi girma tun shekarun
1940.
Manufar wannan matakin dai ita ce kai labarai na
gaskiya da babu son rai a ciki ga karin miliyoyin
mutane a sassa daban-daban na duniya ciki har
da kasashen da 'yancin kafafen watsa labarai ke
fuskantar barazana.
Haka ma sashen na BBC World Service zai
fadada kafofinsa na isar da sakonni ga masu
kallo da saurarensa ta shafukkan internet da na
sada zumunta.
Sashen dai zai bude wasu sabbin sassa da zu
rika watsa shirye-shirye a cikin harsuna 11; abin
da zai kai adadin harsunan da yake watsa shirye-
shiryensa a ciki zuwa 40.
Sabbin harsunan sune na Afaan Oromo, da
Amharic, da Gujarati, da Igbo, da Koriyanci, da
Marathi, Turancin fijin, Punjabi, Telugu, Tigrinya,
da kuma Yarubanci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "BBC za ta bude sabbin sassan harsuna 11"

Post a Comment