Nasri: Guardiola na hana 'yan wasa jima'i

Dan wasan kasar Faransa Samir Nasri ya
bayyana daya daga cikin sirrin nasarar Pep
Guardiola, inda ya ce, kociyan yana hana 'yan
wasansa jima'i ne da dare.
Nasri ya sheda wa tashar talabijin ta Faransa,
cewa kocin dan Spaniya yana ba wa 'yan wasa
umarnin ka da su yi jima'i bayan karfe 12 na
dare.
Dan wasan na Manchester City, wanda ya tafi
Sevilla aro ya ce kocin yana sa wannan doka ne
ko da kuwa babu wani wasa da kungiyarsa za ta
yi washegari, domin 'yan wasan su samu barci
sosai.
Hatta Lionel Messi ma, wanda ake dauka kusan
gwarzon dan wasan duniya, kocin ba ya ware shi
daga wannan doka, a lokacin yana Barcelona.
Nasri ya ce saboda haka ne ma Messin ba ya jin
raunin da ya shafi jijiya ko tsoka

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nasri: Guardiola na hana 'yan wasa jima'i"

Post a Comment