'Yan Niger Delta Avengers sun sake fasa bututan mai

Rahotanni daga Najeriya na cewa mayakan
yankin Naija Delta sun sake fasa bututan mai
guda uku a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na AP da AFP sun
ambato mazauna yankin na cewa an fasa
bututan man ne da ke da tazarar kilomita 100
tsakaninsu ranar Talata da daddare.
Wannan dai shi ne karo na biyar da mayakan ke
fasa bututan man a cikin wata daya duk da tayin
sulhun da Shugaba Muhammadu Buhari na kasar
ya yi musu.
Kungiyar Niger Delta Avengers ta ce ta kai hari a
kan bututan da ke daukar gangar mai 300,000
daga Nembe zuwa tashar Bonny wacce kamfanin
Shell ya mallaka.
Wani shugaban yankin Stephen Igwe ya ce an
kai hare-hare a kan bututan mai na Tebidaba-
Brass mallakin kamfanin Agip.
A farkon watan nan ne mayakan suka kai hare-
hare kan tashar Trans Forcados.
Sun yi zargin cewa ba da gaske gwamnati take
ba a kokarin da take yi na ci gaban yankin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Niger Delta Avengers sun sake fasa bututan mai"

Post a Comment