FA ta sake tukumar Mourinho

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta tuhumi
kociyan Manchester United, Jose Mourinho, a
karo na biyu a cikin mako daya.
Tun farko hukumar ta tuhumi Mourinho kan
kalaman da ya yi kan alkalin wasa Anthony
Taylor, wanda ya shugabanci karawar da United
ta ziyarci Liverpool a gasar Premier.
Yanzu kuma ta sake tuhumar kociyan da laifin
fadin kalaman batanci ga alkalan wasan da Man
United ta tashi babu ci da Burnley a gasar
Premier.
An bai wa Mourinho zuwa ranar Juma'a domin
ya kare kansa, kuma watakila hukumar ta dauki
matakin jan kunne ko cin tara ko dakatar da shi
halartar wasan kungiyarsa zuwa wani lokaci.
United tana mataki na takwas a kan teburin
Premier, kuma ta kasa cin wasa a cikin fafatawa
hudu da ta yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "FA ta sake tukumar Mourinho"

Post a Comment