Koriya ta Kudu: Park na binciken aminiyarta

Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye,
ta sauya Firaiminista da Ministan kudin
gwamnatin ta, a kokarin kaucewa danbarwar
siyasa da ta hada da wata aminiyarta.
Ana zargin kawar ta mai suna Choi Soon-sil, da
kokarin amfani da ita dan cimma manufar samun
kudade, kuma tuni aka tsare ta saboda gudun kar
ta yi kokarin tserewa daga kasar.
Wakilin BBC yace shugaba Parka na cikin tsaka
mai wuya saboda masu shigar da kara sun
gurfanar da kawar ta da suka shafe shekaru 40
tare gaban kuliya, ana tuhumar ta da ko ta na
amfani da kawancen da ke tsakanin ta da
shugabar kasar ta hanyar samun kudade daga
kamfanonin.
Wakilin ya kara da cewa ba a bayyana ko
ministocin an sallame su daga bakin aiki ba, ko
kuma su ne suka zabi barin aiki, ko kuma an
same su da hannu a badakalar da ta taso ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Koriya ta Kudu: Park na binciken aminiyarta"

Post a Comment