Wanda ya sassaka kofin duniya na kwallon kafa ya mutu

Mutumin da ya tsara ya kuma sassaka kofin
duniya na gasar kwallon kafa, Silvio Gazzaniga,
ya mutu yana da shekara 95 a Milan ta Italiya.
Gazzaniga wanda ake yi masa lakabi da Mai
kofuna shi ne ya zana kofin Zakarun Turai da na
Europa.
Shi ne kuma wanda ya kera kofi mai nauyin kilo
shida da aka bai wa Brazil na din-din-din wanda
ake kira Jules Rimet, bayan da ta ci kofin duniya
na uku a shekarar 1970.
Mutane 53 ne suka yi takarar neman aikin
zanawa da sassaka wa hukumar kwallon kafa ta
duniya kofin duniya a shekarar 1971, inda ta zabi
aikin Gazzaniga, wanda ya zana mutane biyu
dauke da duniya a kafadarsu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wanda ya sassaka kofin duniya na kwallon kafa ya mutu"

Post a Comment