Firai Ministan Jamhuriyar Dumukuradiyyar Congo ya yi murabus

Firai Ministan Jamhuriyar Dumukuradiyar Congo,
Augustin Matata Ponyo, ya yi murabus domin
bayar da dama ga wani daga cikin jiga-jigan
'yan hamayya.
Hakan dai na daga cikin wata yarjejeniyar da aka
cimma a tattaunawar watan da ya wuce da ke
nufin kawo karshen rikicin siyasar kasar.
Karkashin yarjejeniyar ana sa ran jinkirta zaben
da aka yi niyyar gudanarwa a cikin watan
Disamba har sai zuwa shekara ta 2018.
Manyan jam'iyyun hamayya dai sun kaurace wa
zaman tattaunawar, suna zargin Shugaba Joseph
Kabila da yunkurin cigaba da mulki.
Mutane da dama ne aka hallaka yayin zanga-
zangar nuna adawa da dage zaben

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Firai Ministan Jamhuriyar Dumukuradiyyar Congo ya yi murabus"

Post a Comment