Nigeria: 'Yan sanda sun yi arangama da 'yan Shi'a a Kano

Akalla mutane takwas aka kashe lokacin da 'yan
sanda suka yi arangama da 'yan Shi'a a wajen
birnin Kano na Nigeria, yayin da aka jikkata 'yan
sanda biyar.
Jami'an tsaro sun ce daya daga cikin 'yan
sandan na nan rai a hannun Allah.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato
wani mutum yana cewa ya ga gawarwakin
mutum goma.
Wani dan jarida da ke tafiya da 'yan Shi'ar ya
shaida wa BBC cewa 'yan sanda sun harbi
mabiyansu da dama, kuma akwai fargabar an
kashe mutane da yawa.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu Yusuf
Ibrahim cewa ya ga motocin 'yan sanda dauke da
mutane hudu da harin ya shafa, amma ba tabbas
ko sun mutu ko suna raye ba.
Kungiyar ta 'yan Uwa Musulmi, wacce ke goyon
bayan kasar Iran, na da tarihin yin fito-na-fito da
jami'an tsaron Nigeria.
Akalla magoya bayanta 349 aka kashe a watan
Disamban bara lokacin wata arangama da suka
yi da sojoji a garin Zaria.
'Yan sanda sun tabbatar da rikicin na baya-bayan
nan, amma kakakinsu a jihar Kano Magaji Majiya
ya ce har yanzu suna tattar bayanai.
Sai dai wani jami'i da bai yarda a bayyana
sunansa ba ya ce sun bude wuta ne saboda 'yan
Shi'ar sun kai musu hari.
Ya kuma kara da cewa ana ci gaba da bata-
kashin.
Yanzu haka an toshe babbar hanyar shiga garin
Kano daga kudu, da kuma fita zuwa babban
birnin kasar Abuja saboda rikicin.
Mabiya Shi'ar na yin tattakin da suka saba yi ne
a duk shekara zuwa garin Zaria, mai nisan
kilomita 165, inda nan ne cibiyar kungiyar ta su

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: 'Yan sanda sun yi arangama da 'yan Shi'a a Kano"

Post a Comment