Ghana: An kai hari gidan jagoran 'yan adawa Akufo Addo

A kasar Ghana, masu gadi da 'yansanda sun
tarwatsa wani gungun jama'a da suka kai wa
gidan jagoran 'yan adawa na kasar hari ranar
Lahadi.
Rahotanni sun ce mutanen sun rika jefa kwalabe
da duwatsu gidan Nana Akufo Addo lamarin da
ya sa har sai da 'yansanda suka rika harbin iska
domin tarwatsa su.
An yi zargin cewa masu harin, magoya bayan
jamiyyar da ke mulkin kasar ne wadanda ke cikin
masu wani tattaki na motsa jiki da suka biyo ta
kofar gidan shugaban 'yan hamayyar wanda ke
takarar shugabancin kasar a inuwar jam'iyyar
NPP.
Amma jam'iyyar mai mulki ta NDC ta musanta
cewa magoya bayan nata ne suka fara kai hari
kan gidan; inda ta ce sun mayar da martani ne
kan harbin gargadi da masu gadin gidan suka yi
lokacin da jerin gwanon masu tattakin ke
wucewa kusa da gidan.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ghana: An kai hari gidan jagoran 'yan adawa Akufo Addo"

Post a Comment