Ana taro a kan sauyin yanayi a Morocco

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari
na Najeriya zai bi sahun sauran shugabannin
kasashen duniya domin halartar taron Majalisar
dinkin duniya kan sauyin yanayi a birnin
Marrakech na Morocco.
A yayin taron, Shugaban zai gabatar da jawabi
kan matsayin kasarsa game da muhimman
batutuwa da suka jibanci sauyin yanayin a ranar
Talata yayin zaman farko na kaddamar da taron.
Kazalika shugaban na Najeriya zai kuma gabatar
da bukatar kasarsa ta samun goyon bayan
kasashen duniya wajen aikin share yankin Ogoni
na Niger Delta da kuma kokarin farfado da tafkin
Chadi.
Anasa ran taron zai hado kan shugabannin
kasashen duniya da ministocin muhalli da
wakilan kungiyoyin sa kai da na 'yan kasuwa
daga kasashe 197, kuma shi ne na farko tun
bayan muhimmiyar yarjejeniyar Paris wadda aka
aiwatar a ranar 4 ga watan Nuwambar da muke
ciki.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana taro a kan sauyin yanayi a Morocco"

Post a Comment