Trump da Clinton duk abu daya ne - Shekau

Shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar
Boko Haram biyu da ake da su a Najeriya ya ce
ko da Hillary Clinton Amurkawa suka zaba a
zaben shugaban kasa na makon jiya sun yi
hasara.
A cikin wani sakon murya da wani makusancinsa
ya aiko wa sashen Hausa na BBC, Abubakar
Shekau ya ce a shirye suke su kalubalanci
manufofin zababben shugaban na Amurka.
Ya kuma yi Allah-wadai da matakin da ya ce
sarkin kasar Saudiyya mai bin tsarin shari'ar
musulunci ya dauka na yin maraba da zaben Mr.
Trump.
Ya yi amfani da wannan damar wajen daukar
alhakin kai munanan hare-hare kan dakarun
Najeriya a wasu sassan jihar ta Borno a
kwanannan wanda ya hallaka da dama daga
cikinsu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Trump da Clinton duk abu daya ne - Shekau"

Post a Comment