Hukumar FIFA ta bayyana sunayen masu horarwa da za’a zabi 1 wanda yafi kwarewa.

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta fito da
sunayen masu horarwa cikin wanda 1 daga
ciki za’a zaba a matsayin mafi kwarewa.
Kyautar za ta kasance in anyi dubo ga irin
rawar da kungiyar ka ko kasar da kake
horarwa ta taka, da cin kofuna da wasu
sauran kyautuka.
An zabi Chris Coleman wanda yaje da kasar
Wales wasa ta kusa da ta karshe tare da
kocin kasar France Didier Deschamps da mai
horar da Portugal Fernando Santos wadan
da suka doka wasar karshe a gasar Euro.
Didier Deschamps
Claudio Reneiri yana cikin wadanda aka zaba
saboda taimaka ma kungiyar shi da yayi da
cin kofin Firimiya Lig.
Ranieri
Sauran masu horarwar firimiya Lig da aka
zaba sun hada da Pochettino na Tottenham
da Jurgen Kopp wanda ya taimaka ma
Liverpool zuwa kwallon karshe ta Uefa da
wasa ta karshe a kofin FA.
An zabi Pep Guardiola tsohon mai horarwa
na Beyern Munich da Diego Simeone wanda
ya kai kungiyar shi matakin buga wasar
karshe a kofin zakarun turai.
Sai Zinadane Zidane wanda ya taimaki
Madrid zuwa matakin cin kofin zakarun turai
na 11.
Zinedine Zidane
Allah ya ba mai rabo sa’a amin…

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hukumar FIFA ta bayyana sunayen masu horarwa da za’a zabi 1 wanda yafi kwarewa."

Post a Comment