Jibrin ya fatsama wa yan mazabarsa da naira miliyan 100

Tsohon shugaban kwamitin dacewa na
majalisa, Abdulmumin Jibrin ya fantsama
wa yan mazabar siyasan sa da kyautan naira
miliyan 100 na sharen fage.

Dan majalisar dokokin na Kano yayi hakan ne
a matsayin wani bangare na ayyuka don cika
kwanaki 100 da fara jihadin yaki da cin hanci
da rashawarsa kan zambar kudin kasafi.
Jibrin ya kuma rarraba Babura, janareto,
kekunan dinki, injinan nuka da sauran
abubuwan karfafawa wanda suka kai kimanin
naira miliyan 100 ya kuma dauki nauyin
karatun dalibai guda 1,000.
Yayinda yake gabatar da abubuwan tallafi ga
mutane 5,000 da suka amfana, Jibrin yace
anyi karamcin ne domin tallafawa yan
mazabar sa sakamakon halin wahala da
kasar ke fama da shi.
Jibrin yace sadaukarwansa don jin dadin
mutanen sa ba wani sabon abu bane, ya
kara da cewa ya dade yana tallafawa
mutanen sa tun kafin ma ya fada harkan
siyasa.
Dan majalisar yace ba zai yi watsi da
gwagarmayar ba har sai an dawo da
nutsuwar tunani a cikin kasafin kudi a kasar
kamar yadda ba zai koma baya a kan
gwagwarmayar yaki da cin hanci da
rashawar da ya fara tun kwanaki 100 da
suka wuce ba.
Ku tuna cewa Jibrin ya zargi kakakin
majalisa, Yakubu Dogara, mataimakin kakakin
majalisa, Yusuf Lasun, Cif Whip Alhassan
Doguwa da sauran mambobin majalisa da yin
aragizon kasafin kudi na shekara 2016.
Kalli hotuna a kasa:




SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jibrin ya fatsama wa yan mazabarsa da naira miliyan 100"

Post a Comment