Bikin cikar Sarkin musulmi shekaru 10 a karagar mulki

A yau 2 ga watan Nuwamba mai alfarma
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad
Abubakar III ya cika shekaru 10 akan
karagar mulki.
Mai alfarma Sa’ad Abubakar shi ne sarki na
20 a jerin sarakan musulunci tun bayan
shehu dan Fodio. A watan Nuwambar 2016
ne aka nada shi Sarki don maye gurbin
yayansa mai alfarma Sarkin Musulmi
Muhammad Maccido daya rasu a hadarin
jirgi a filin tashin jirgi dake garin Abuja.
Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar
Mai alfarma ya kasance wata hanyar kulla
alaka tsakanin Musulmai da wadanda ba
musulmai ba saboda kaunar sa na ganin
zaman lafiya ya dawwama a kasar nan.
yayin da yake yaba mai alfarma, gwamnan
jihar Imo Rochas Okorocha yace “zancen
kokarin hadin kan kasar nan da zamanta
cikin lafiya ba zai taba kammaluwa ba tare
da an ambaci sunan mai alfarma sarkin
musulmi ba.
“Sultan mutum ne daya dage
wajen yada zancen zama lafiya a tsakanin
mu, tare da yin duk mai yiwuwa don hada
kan al’umomin kasar nan”
Shi ma Kaakakin majalisar wakilai ba’a barsa
a baya ba wajen yabawa ma Sultan, yace
“Sultan a matsayinsa na shugaban gargajiya,
yayi kokarin kawo kyakyakyawan
zamantakewa tsakanin addinan kasar nan
daban daban, tare da kawo zaman lafiya a
kasa”
A shekarar 2012 ne jaridar Leadership ta
karrama Sultan da lamabar yabo ta gwarzon
shekara tare da shugaban kungiyar addinin
kirista ta Katolika John Onaiyekan. Sa’annan
sunan Sultan ya sha shiga jerin mutane
musulmai da suka fi shahara a duniya gaba
daya.
Ga kada daga cikin mukamen da mai alfarma
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar
ke rike dasu:
Shugaban majalisar koli ta harkokin
musulunci
Shugaban Jama’atu Nasril Islam
Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na
yankin Arewacin kasar nan
Shugaban majalisar sarakunan gargajiyan
kasar nan
Shugaban Hadaka na majalisar addinan
kasar nan.
Allah ya ja zamanin Sarkin musulmi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Bikin cikar Sarkin musulmi shekaru 10 a karagar mulki"

Post a Comment