Ingila za ta karbi bakuncin Spaniya

Tawagar kwallon kafa ta Spaniya za ta ziyarci ta
Ingila a wasan sada zumunta da za su fafata a
ranar Talata a Wembley.
Kasashen biyu sun kara a manyan wasanni har
sau 24, Ingila ta samu nasara a karawa 12,
Spaniya ta ci wasanni tara, suka yi canjaras a
fafatawa uku.
Karawar karshe da kasashen suka yi a wasan
sada zumunta, Spaniya ce ta samu nasara da ci
2-0 a kan Ingila a ranar 13 ga watan Nuwambar
2015.
A ranar Juma'a Ingila wadda ke mataki na 12 a
jerin kasashen da suke kan gaba wajen murza-
leda a duniya ta doke Scotland da ci 3-0 a wasan
shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a
Wembley.
Ita kuwa Spaniya wadda ke matsayi na 10 a
jadawalin Fifa da ta fitar na wadanda ke kan
gaba a fagen tamaula a duniya, doke Macedonia
4-0 ta yi a ranar Asabar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ingila za ta karbi bakuncin Spaniya"

Post a Comment