Nigeria: Farashin kayan masarufi na kara hauhawa

Hukumar kididdiga ta kasa ta ce farashin kaya a
Najeriya ya karu da kusan sama da kashi 18
bisa dari a cikin watan Nuwamba.
Ta ce farashin kayan ya yi tashin gwauron zabin
da bai taba yi ba a cikin shekaru 11, wanda
hakan wata alama ce ta karin matsin tattalin
arziki a kasar.
Farashin da ya fi tashi shi ne na gidaje, da ruwan
sha, da wutar lantarki, da na gas, da sauran
makamashi, in ji hukumar.
Shi ma farashin kayan abinci ya tashi zuwa
sama da kashi 17 cikin dari a watan Oktoba, idan
aka kwatanta da kashi 16 da rabi a watan
Satumba.
Najeriyar wacce memba ce a kungiyar kasashe
masu arzikin man fetur OPEC, kuma mafi girman
arziki a Afirka, na fuskantar matsin tattalin arziki
mafi muni a cikin shekaru 25.
Faduwar farashin mai da yawan kai hare-hare
kan bututan man a yankin Niger Delta na haifar
da koma baya na danyen man da kasar ke
hakowa.
Ya kuma haddasa karancin dalar Amurka, da
hakan ya yi mummunan tasiri kan harkokin
kasuwancin shigowa da kayayyakin ciyar da
masana'antu a kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Farashin kayan masarufi na kara hauhawa"

Post a Comment