Klose ya yi ritaya daga buga tamaula

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Jamus,
Miroslav Klose, ya yi ritaya daga murza-leda.
Tsohon dan kwallon Bayern Munich, ya taimaka
wa Jamus lashe gasar cin kofin duniya a 2014.
Kuma ya karbi kyautar wanda ya fi cin kwallaye
a tarihin gasar gaba daya, bayan da ya zura
kwallo 16 jumulla a wasannin da ya halarta na
lokaci daban-daban.
Klose wanda ya ci kofuna biyu na gasar
Bundesliga a Bayern Munich, ya zauna ba shi da
kungiyar da yake buga tamaula, bayan da
yarjejeniyarsa ta kare da Lazio a karshen kakar
bara.
Dan wasan wanda aka haifa a Poland ya yi wa
Jamus wasanni 137, inda ya shafe tarihin yawan
cin kwallaye da Gerd Muller ya kafa tsawon
shekara 40 da cin kwallaye 68 a Yunin 2014.
Klose ya yi ritaya daga buga wa Jamus tamaula
bayan da aka kammala gasar cin kofin duniya a
Brazil a shekarar 2014, ya kuma ci wa tawagar
kwallaye 71.
Yanzu haka yana shirin komawa cikin kociyoyin
tawagar kwallon kafa ta Jamus, bayan da
Joachim Low ya mika masa goron gayyata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Klose ya yi ritaya daga buga tamaula"

Post a Comment