Pakistan ta ce india ta kashe sojojinta 7

Rundunar sojin Pakistan ta ce sojojinta bakwai
sun mutu a wani luguden wuta da dakarun India
suka yi a yankin Kashmir da kasashen ke
takaddama a kansa.
Babban hafsan sojin kasar Pakistan din Raheel
Sharif da sauran jami'ai sun gudanar da sallar
jana'izar sojojinta da aka hallaka a wata musayar
wuta a kan iyaka
Wasu rahotanni sun ce wannan ita ce asarar
rayuka mafi muni a yankin na Kashmir da
Pakistan din ta yi a lokaci guda tun bayan
yarjejeniyar shekara ta 2003.
Kasashen India da Pakistan na zargin junansu da
karya yarjejeniyar tsagaita wutar ta shekara ta
2003.
Tashin hankalin ya ta'azzara kan dadadden
rikicin tun bayan kai wani hari kan sansanin sojin
India a cikin watan Satumba.
Duka bangarorin sun ba da rahoton kashe musu
fararen hula da dama, ko kuma jikkata a
makonnin baya, lokacin da aka yi ta ba-ta-kashi a
yankin.
Daruruwan fararen hula ne a kauyukan da ke
kusa da yankin da ake takaddamar a kai aka
kwashe, domin kare su.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Pakistan ta ce india ta kashe sojojinta 7"

Post a Comment