Obama na kokarin kau da fargabar kasashe game da Trump

Shugaban Amurka mai-barin-gado Barack
Obama na kokarin tabbatar wa kasashe kawayen
Amurka cewa Donald Trump zai mutunta
kawance daban-daban da kasar ke ciki idan ya
karbi mulki a watan Janairu.
A yayin wani taron manema labarai gabanin
tafiyarsa ta karshe zuwa wata kasar waje a
zaman shugaban kasa, Mr. Obama ya ce Mr.
Trump ya nuna sha'awar ci gaba da kasancewar
Amurka a kungiyar NATO.
A lokacin yakin neman zabe dai Donald Trump ya
jefa shakku a zukatan kawayen Amurka na ko
zai bar kasar ta ci gaba da zama a kungiyar ta
NATO idan ya ci zabe, yana mai nuna bacin
ransa ga yadda kasashen da dama da ke cikin
kawancen ba su kashe kashi 2% na kudaden
shigarsu kan tsaro- wanda sharadi ne ga
zamowar kasa wakiliya a kawancen.
Amma shugaba Obama wanda ke kan hanyarsa
ta ziyartar kasashen Jamus da Girka da kuma
Peru ya ce daya daga cikin muhimman ayukkan
da zai yi yayin wannan ziyarar shi ne bayar da
tabbacin cewa Mr. Trump na goyon bayan zaman
kasar a kungiyar ta NATO.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Obama na kokarin kau da fargabar kasashe game da Trump"

Post a Comment