Yara na fuskantar matsanancin karancin abinci a Najeriya- Save the Children

Kungiyar agaji ta Save the children ta ce
matsalar karancin abinci mai gina jiki ta yi
kamari a tsakanin yara 'yan kasa da shekaru
biyar da ke yankin arewa-maso-gabashin
Najeriya.
A wata sanarwar da kungiyar ta fitar, kungiyar ta
kuma bayyana fargabar cewa akalla yara 200 za
su iya rasa rayukansu a kullum saboda tsananin
yunwa.
Kungiyar ta ce binciken da ta gudanar daga
watan Yunin da ya gabata zuwa watan Oktobar
da ya wuce, ya nuna cewa kimanin kashi 40
zuwa 50 cikin dari na yara 'yan kasa da shekarar
biyar ne ke fuskantar matsanancin karancin
abinci mai gina jiki a wasu sassan arewa maso
gabashin Najeriya.
Kungiyar ta save the children ta dora alhakin
halin da yaran ke ciki ne a kan matsalar tsaro da
kuma karancin kayayyakin agaji.
Najeriya ta kwashe tsawon shekaru bakwai tana
fama da rikicin Boko Haram, lamarin da ya janyo
asarar dubban rayuka ya kuma daidaita miliyoyin
mutanen yankin da gidajensu, inda suka zamo
'yan gudun hijira.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Yara na fuskantar matsanancin karancin abinci a Najeriya- Save the Children"

Post a Comment