Russia: An cafke ministan tattalin arziki kan cin hanci

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar
Russia SK ta cafke ministan harkokin tattalin
arziki na kasar Alexei Ulyukayev.
Hukumar ta SK ta ce ministan ya karbi cin
hancin dala miliyan biyu.
Mr Ulyukayev shi ne mai rike da mukami mafi
girma a kasar ta Rasha da aka taba cafkewa tun
bayan yunkurin juyin mulki a shekara ta 1991.
Hukumar ta ce ya yi ''barazanar'' hana ruwa gudu
ga ayyukan kamfanin mai na kasar Rosneft
lokacin da ya karbi kashi 50 bisa dari na ayyuka
a daya kamfanin mai na kasar Bashneft.
Kakakin hukumar ta SK Svetlana Petrenko, ta ce
"an kama Ulyukayev da hannu dumu-dumu'', yana
karbar dala mliyan biyu a ranar 14 ga watan
Nuwamba don ya amince da bukatun kamfanin
na Rosneft.
Cafke Mr Ulyukayev ya zama wani babban labari
a gidan talabijin na kasar ta Russia, da aka yiwa
take ''Yaki ta cin hanci da rashawa''.
Idan dai aka same shi da aikata laifin zai
fuskanci zaman gidan yari na shekara takwas
zuwa 15.
A shekara ta 2004 ya zama shugaban babban
bankin kasar ta Rasha.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Russia: An cafke ministan tattalin arziki kan cin hanci"

Post a Comment