Pacquiao ya koma fagen dambe

Dan damben boksin Manny Pacquiao ya koma
fagen dambe inda kuma ya doke zakaran
damben Jessie Vargas kana ya lashe gasar WBO
a Las Vegas.
A watan Afrilu ne tsohon gwarzon dan damben
duniyar na rukuni na takwas din, mai shekara 37,
ya bayyana cewa ya daina dambe bayan ya doke
Timothy Bradley.
Pacquiao ya zama dan majalisar dattawa a
kasarsa Phillipines.
Sai dai ya ce ya koma fagen dambe ne "domin
shi ne babban abin na fi so a rayuwata."
Alkalan wasan sun ce ya yi nasara da ci
114-113, 118-109 da kuma 118-109.
Tsohon abokin karawarsa Floyd Mayweather Jr
na wurin da ya lashe gasar.
Mayweather ya ce Pacquiao ya yi rawar gani,
yana mai jinjina masa bayan an kammala wasan.
Mayweather ne dai ya doke Pacquiao inda ya
zama gwarzon dan damben boksin na duniya a
watan Mayun shekarar 2015 a fafatawar da ake
yi wa lakabi "babban karon-battar wannan
zamani".
Pacquiao ya ce shi ne ya gayyaci Mayweather
domin halartar wurin damben da ya yi, kuma da
aka tambaye shi ko za su sake fafatawa sai ya
ce "za mu gani."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Pacquiao ya koma fagen dambe"

Post a Comment