Hadiza Gabon ta ci gasar Africa Films Awards

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood Hadiza
Aliyu, wacce aka fi sani Hadiza Gabon ta lashe
kyautar 'yar wasan da ta fi tallafawa babban
jarumi a fim a bikin bayar da kyautar Africa
Films Awards na shekarar 2016.
Bikin, wanda aka yi ranar Asabar da almuru a
birnin London ya kuma karrama Jamilu Yakasai
da Uzee Concept.
Wadanda suka hada bikin sun ce Hadiza Gabon
na daya daga cikin jaruman Kannywood da suka
fi shahara kuma ana yin koyi da ita saboda tana
riko da al'adunta da yin shiga mai kyau.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram,
'yar wasan ta ce ta sadaukar da kyautar ga
magoya bayanta da kuma Ali Nuhu bisa
taimakonta da yake yi.
Uzee Concept dai ya lashe kyautar gwarzon mai
hada fina-finai na shekarar 2016.
Ali Nuhu da dan majalisar wakilan Najeriya
wanda aka dakatar, Abdulmumini Jibrin na cikin
wadanda suka halarci bikin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hadiza Gabon ta ci gasar Africa Films Awards"

Post a Comment