Garkuwan Alabo ya buge Mahaukaci Teacher

Garkuwan Shagon Alabo ya yi nasarar buge
Shagon Mahaukaci Teacher a dambatawar da
suka yi a gidan damben Ali Zuma a ranar Lahadi
da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.
Garkuwan Shagon Alabo dan damben Kudu ya
buge Shagon Mahaukacin Teacher ne daga
Arewa a turmin farko da suka taka damben.
Tun farko Shagon Bahagon Falgore ne daga
Kudu ya buge Shagon Autan Fafa daga Arewa a
turmin farko.
Shi ma Shagon Shagon Mada daga Kudu buge
Shagon Buzu daga Arewa ya yi, da farko Shagon
Buzu bai amince da kisan farko ba, suka sake
takawa dambe aka kara buge shi a karo na biyu.
Ga sauran wasannin da aka yi babu ci:
Shagon Shagon Dan Kanawa daga Kudu da
Garkuwan Bhagaon Balan Gada daga Arewa
Shagon Caka-Caka daga Arewa da Autan
Faya daga Kudu
Dodon Dan Jamilu daga Arewa da Bahagon
Sisco daga Kudu
Dogon Minsta daga Kudu da Autan Fafa
daga Arewa
Autan Faya daga Kudu da Bahagon Abba
daga Arewa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Garkuwan Alabo ya buge Mahaukaci Teacher"

Post a Comment