An bude katafariyar gadar sama a Accra

An bude sabuwar katafariyar gadar sama mai
rassan titina, a Accra, wadda ake sa ran za ta
kawo karshen wahalar da ake sha kullum ta
cunkoson ababan hawa a babban birnin na
Ghana.
Shugaba John Mahama, wanda ya bude gadar,
wadda aka sanya wa sunan Kwame Nkrumah
(Kwame Nkrumah Interchange), ya ce, ita ce
gadar sama mafi tsawo da nisa a duk yammacin
Afirka.
A tsakiyar katafariyar gadar wadda kafar labaran
Joy News ta ce an kwaikwayo ta ne daga Dubai,
an gina wani wurin shakatawa da ruwa ke tsiri
yana sauka, mai kayatarwa da ban sha'awa.
A yayin bude gadar Shugaba Mahama ya ce, ''ba
wai hanya ce kawai ta zamani ba, wuri ne mai
kyau ga 'yan yawon bude idanu.''
Ya kara da cewa, ''lafiya da kuma farin cikin 'yan
kasar abubuwa ne da su ma su ke da
muhimmanci.''
Shugaban ya bukaci jama'a da su rika zuwa
wannan wurin shakatawa da ke tsakiyar gadar
domin hutawa da nishadi.
Aikin wanda ya dauki shekara uku kafin a
kammala shi, ya kunshi titunan sama da dama
da suka hada yankin tsakiyar babban birnin, mai
fama da cunkoson ababan hawa da jama'a, da
sauran sassan birnin.
Tsawon shekaru jama'a ke fama da matsalar
cunkoson ababan hawa, lamarin da ke bata musu
lokaci a kullum

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An bude katafariyar gadar sama a Accra"

Post a Comment