'Yan Niger Delta sun mika bukatunsu ga gwamnati

Dattawan yankin Niger Delta a Nigeria sun
gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari
shawarwari 16 da suka ce za su taimaka wurin
samar da zaman lafiya a yankin.
A ranar Talata ne shugaban ya gana da wakilan
masu tayar da kayar baya da kuma shugabannin
al'umma da nufin kawo karshen hare-haren kan
bututan mai a yankin.
Shugaban ya shaida wa tawagar cewa matsalolin
da gwamnatinsa ta tarar a lokacin da ta karbi
mulki suna da yawan gaske, wadanda suka hada
da faduwar farashin mai, da kasa biyan albashi a
jihohi 27 daga cikin 36 na kasar.
Sauran matsalolin a cewar shugaban Najeriyar
sun hada da rashin tattalin dan abun da kasar ke
samu, lamarin da ya ce babu yadda za a yi a ci
gaba da tafiya a haka.
Hare-haren kungiyoyi irin su Niger Dealta
Avengers sun taimaka wajen kassara tattalin
arzikin kasar.
Jerin bukatun da tawagar ta gabatar sun hada da
gaggauta kammala manyan hanyoyin da aka fara
a yankin da kuma mayar da hedkwatar manyan
kamfanonin mai a Nigeriar zuwa yankin Niger
Delta, matakin da a cewarsu zai taimaka wajen
kara samar da ci gaba a yankin.
Shugabannin yankin Niger Deltan karkashin
jagorancin Chief Edwin Clerk sun kuma bukaci
gwamnatin tarayya da ta gaggauta share
dagwalon mai da ya mamaye wasu garuruwa a
yankin baya ga yankin Ogoni.
Haka kuma Shugabannin sun nemi gwamnati da
ta sake duba shirin afuwa ga tsagerun yankin
tare da tabbatar da cewa an samar da ayyukan
yi ga wadanda aka horas da su karkashin shirin
yin afuwa ko kuma a rika ba su dan abun hasafi.
Sun kuma sha alwashin ci gaba da tattaunawa
akai-akai a jihohi daban-daban na yankin a wani
mataki na ganin an samu dorewar zaman lafiya.
Sannan suka ce tuni aka fara ganin tasirin
tattaunawar da suke yi tsakaninsu wanda hakan
ya kai ga yanzu aka samu karuwar danyen mai
da ake hakowa zuwa sama da ganga miliyan
biyu.
Shugaba Buhari wanda ya ce yana jiran rahoton
wani kwamitin da ya dora wa alhakin sake nazari
a kan shirin yin afuwa ga tsegurun yankin Neja
Delta, inda daga nan ne gwamnatin sa za ta ga
bangaren da ta gaza domin yin gyara.
Tawagar karkashin kungiyar Pan Niger Delta
Forum ta kuma jaddada goyon bayanta ga
Shugaba Buhari bisa abin da ta ce kokarin
gwamnatinsa wajen tabbatar da hadin kan
al'ummar Nigeria a matsayin kasa daya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Niger Delta sun mika bukatunsu ga gwamnati"

Post a Comment