Mutane 18 sun mutu a rikici tsakanin Fulani da Manoma a Niger

A Jamhuriyar Niger, a kalla mutane 18 ne suka
mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a wani
kazamin fada daya barke tsakanin manoma da
makiyaya a jahar Tawa.
Jami'ai sun ce rikicin ya barke ne kusa da wani
kauye mai suna Bangui, da ke kudancin kasar.
Monoman dai na zargin Fulanin da barin
dabbobinsu shiga wasu gonaki tare da lalata
musu amfanin gona.
Rikici akan gonaki da sauransu tsakanin Fulani
makiyya da manoma ya zama tamkar ruwan dare
a kasashen yammacin Afirka, lamarin da kan kai
ga asarar rayuka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mutane 18 sun mutu a rikici tsakanin Fulani da Manoma a Niger"

Post a Comment