El-Rufai ya sasanta rikicin masallacin Sultan Bello

Bangarorin da ke rikicin shugabanci a kan
masallacin Sultan Bello da ke Kaduna sun
sasanta bayan da gwamnatin jihar ta shiga
tsakani.
Matakin da gwamnan jihar ya dauka shi ne na
cewa a bar mataimakin limamin ya ci gaba da
limanci a matsayin wucin-gadi kafin a nada
limami na din-din.
Kwamitin masallacin bisa hadin guiwa da Sarkin
Zazzau, Alhaji Shehu Idris, da kungiyar Jama'atu
Nasril Islam da bangaren Dakta Ahmad Gumi da
sauran masu ruwa da tsaki su aka dora wa
alhakin nada sabon limamin.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar,
Samuel Aruwan, ya fitar, ya ce, an kawo karshen
rikicin ne bayan wani zama da bangarorin suka yi
a gidan gwamnati, wanda gwamnan jihar Nasir
Ahmad El-Rufai ya shirya.
Sanarwara ta ce bayan da gwamnan ya ji
bayanin dukkanin bangarorin da ke rikicin, ya ce
gwamnati ta shiga tsakani ne saboda tsaro
kawai, amma ba domin wani abu ba.
Sannan ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta
lamunta da duk wani mataki na karya doka ba da
sunan addini, da kuma barin mutane suna nema
wa kansu mafita ba kan wata matsala.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "El-Rufai ya sasanta rikicin masallacin Sultan Bello"

Post a Comment