Za’a kammala aikin hanyar Legas-Ibadan, inji Fashola

Ministan aiki da, lantar da gidaje Babatunde
Raji Fashola yace nan bada dadewa ba za’a
kammala aikin fadada babban titin Legas
zuwa Ibadan.
Babatunde Fashola
Jaridar The Nation ta ruwaito Fashola yana
bayyana haka a lokacin dayake bada bahasin
yadda ya tafiyar da akalar ma’aikatarsa cikin
shekara guda daya kwashe a matsayin
minista.

Ministan yace za’a rufe katafaren gadar dake
kan iyakar jihohin Legas da Ogun saboda
aikin da ake gudanarwa a yankin.
Idan aka kyale hanyoyi haka, zasu dinga
lalacewa ne, don haka akwai bukatar
gyaransu da yi musu kwaskwarima akai akai,
nji Fashola.
Fashola ya kara dacewa gwamnati na duba
yiwuwar dakatar da manyan ababen hawa
daga bin titunan, sakamakon nauyinsu yayi
ma titin yawa. Sa’annan yace kamata yayi a
gina sabbin gidan ajiye manyan ababen hawa
don rage nauyin da manyan motoci ke
dauka.
A wani labarin kuma hukumar kare haddura
a kasa (FRSC) ta bayyana cewar zata
karkatar da matafiya masu fitowa daga
Legas zuwa Ibadan zuwa hanyar Ibadan
zuwa Legas sakamakon aikin hanyar.
Hakan zai sanya rufe hanyar Legas zuwa
Ibadan, zuwa Sagamu. Hanyar zai kwashe
kwanaki bakwai a rufe, daga 16 ga watan
Nuwamba zuwa 23.
Sa’annan hukumar tace
kamfanin Julius Berger zata rufe wani
bangare na babban titin Ibadan-Legas.
Matafiya da dama sun nuna damuwarsu
dangane da rufe hanyar, amma hukumar
FRSC ta sake fitar da wata sanarwa inda
take baiwa jama’a tabbacin hana cunkoso a
kan hanyar duk da aikin dake gudana.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Za’a kammala aikin hanyar Legas-Ibadan, inji Fashola"

Post a Comment