Ta fado daga bene hawa 9, bayan sharholiya da Saurayinta

Wata budurwa yar kasar Birtaniya ta fado
daga wani dogon benen gidan hutawa bayan
sun hole da saurayinta.
Hall da benen da ta fado
Budurwar mai suna Danielle Hall ta fado ne
daga hawa na 9 na wani gidan shakatawa
mai suna Bermuda dake garin Benidorm na
kasar Sifen bayan sun sha sharholiya da
saurayinta.
Ita dai Hall ta fita da saurayinta ne zuwa
wurin shakatawa dake gabar tekun Costa
Blanca tare da saurayinta dan shekaru 23
mai suna Jordan, gabanin mutuwarta.
Rahotanni sun bayyana cewar masoyan sun
sha barasa sunyi tatil bayan sun sha
sharholiya, cikin mayen barasa ne Hall ta
fara tangali tangal, sai kawai ta fado daga
hawa na 9 na benen, lamarin ya faru ne da
misalin karfe 9 na safe, koda aka kira
yansanda ta rigaya tace ga garinku nan.
Rahotanni sun bayyana cewar kakar Hall ita
ma ta kama daki a gidan hutawar,
sakamakon sun yi niyyar kwashe mako guda
suna shakatawa ne a gabar tekun.
Wata majiya ta bayyana mana cewar,
ma’aikatan gidan hutawar sunyi matukar
kaduwa da farywar lamarin. Ita kanta
ma’aikaciyar data baiwa Hall dakin da take
zaune a ciki ta tsargu, inda aka jiyo ta tana
kuka tana fadin idan da ta basu daki a hawa
na 1 ko na 2 da Hall bata mutu ba.
Dayake majiyar tamu ta ga lokacin da Hall
ke fadowa daga benen, tace ta gagara barci
tun lokacin da lamarin ya faru. Yansanda sun
yi ma shaidun gani da ido tambayoyi, tare da
saurayin Hall da kakarta. Sa’annan
yansandan sun ce mutuwar yafi kama da
hadari ba daukan rai ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ta fado daga bene hawa 9, bayan sharholiya da Saurayinta"

Post a Comment