Gwamnatin Shugaba Buhari ta amince a karo Jami’o’i

– Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari
za ta amince da kirkiro sababbin Jami’o’i a
fadin Tarayyan Kasar
– Duk Jami’o’in da za a karo na kasuwa ne,
ba na Gwamnati ba
– Gwamnatin tarayya ta yanke wannan
shawarar ne a zaman da ta yi na yau
A zaman majalisar zartarwa na tarayyar
Kasar watau FEC na Yau,
 gwamnatin
Shugaba Buhari ta amince da kirkiro
sababbin Jami’o’i a fadin Kasar nan har
guda 8.
Gwamnatin Shugaba Buhari ta dauki wannan
mataki ne a zaman Majalisar zartarwa na
mako-mako da tayi a Fadar Gwamnati da ke
Birnin Abuja.
A taron da aka yi a Aso Rock, Gwamnatin
Shugaba Buhari tayi na’am da karo sababbin
Jami’o’i guda 8 a fadin Najeriya. Sai dai kaf
wadannan Jami’o’i ban a Gwamnati bane,
watau na ‘yan kasuwa ne.
Shugaba Buhari ya jagoranci wannan taro da
shi da Ministocin sa tare da sauran
mukarraban Gwamnatin Tarayya. Sababbin
Jami’o’in sune; Jami’ar Anchor a Legas,
Jami’ar Clifford, Jami’at Coal City, Jami’ar
Dominican, Jami’ar Kola Daisi, Jami’ar
Legacy dsr.
Haka kuma a yau Kungiyar Kwadago ta Kasa
watau NLC, za ta zauna da Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari. Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari zai gana da Kungiyar
Kwadago ta Kasa NLC, da kuma Kungiyar
‘Yan Kasuwan Najeriya watau TUC domin
ganin Shugaba Buhari ya kara albashin
ma’aikata daga N18000 zuwa akalla N56000
a kowane wata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gwamnatin Shugaba Buhari ta amince a karo Jami’o’i"

Post a Comment