Donald Trump abokin tafiyarmu ne - Assad

A kalamansa na farko kan manufofin Amurka
tun bayan zaben Donald Trump, Shugaban Syria
Bashar Al - assad ya ce shugaban mai-jiran-
gado ka iya zama abokin tafiya ga kasarsa
wajen yaki da ta'addaci.
Sai dai shugaban na Syria ya ce zai jira ne ya ga
kamun ludayin Mr. Trump in har zai iya cika
alkawarin da ya yi na yakar ta'addanci
kasancewar bai taba rike mukaminsa siyasa ba a
baya.
''A wurinmu dai har yanzu abin na a cikin duhu
na ko zai iya cika alkawurran da ya yi ko kuma
a'a. Wannan ne ya sa muke kafa-kafa wajen
daukar wata matsaya a kansa musamman
saboda bai taba rike mukamin siyasa ba a baya.
''
Shugaba Assad ya ce kodayake ba zai ce komai
ba tukuna kan ko shugaban mai-jiran-gado zai
iya kawo sauyi a manufar Amurka kan kasarsa ,
yana fatan Amurka ta kasance ''mai adalci, da
mutunta dokokin kasa da kasa, kuma bugu da
kari ta daina mara wa 'yan ta'adda baya a Syria.''
A lokacin yakin neman zaben sa dai Donald
Trump ya sha alwashin ruguza kungiyar IS, yayin
da ya yi Allah-wadai da manufar gwamnatin
Obama ta mara wa 'yan tawayen na Syria baya

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Donald Trump abokin tafiyarmu ne - Assad"

Post a Comment