Majalisa ta yi watsi da sunayen jakadan da Buhari ya aika

Majalisar dattawan Najeriya ta kada kuri'ar kin
amincewa da sunayen jakadu 46 da shugaba
Buhari ya aike mata don tantancewa.
Yan majalisar sun ce za a sake mayar wa da
shugaba Muhammadu Buhari sunayen " domin ya
yi musu garanbawul''
Shugaban masu rinjaye na majalisar Ali Ndume
ne ya gabatar da bukatar mayar da sunayen ga
shugaba Buharin, yayin da shugaban marassa
rinjaye, Godswill Akpabio na PDP ya mara masa
baya.
Sun ce sun samu koke-koke da dama kan tsarin
da aka bi wajen zabo sunayen wadanda za a bai
wa mukamin jakadun Najeriyar a kasashen waje.
Wasu daga cikin sanannun da sunayensu ke ciki
akwai tsohon alkalin kotun kolin kasar Justice
George Oguntade; da Yusuf Tugar daga jihar
Bauchi, da Mohammed Hayatuddeen daga jihar
Borno, da Jamila Ahmadu-Suka daga jihar
Sokoto.
Gwamnonin jihohi sun nuna rashin jin dadinsu
kan rashin tuntubar su da shugaba Buharin ya yi
cikin wadanda za su zabi jakadun, inda suka ce
mutanen ba 'yan siyasa ba ne.
A ranar 20 ga watan Oktoba ne Buharin ya aike
wa da majalisar dattawan wasikar neman
amincewa da sunayen mutanen 46 da suka hada
da Olorunmimbe Mamora da Dakta Usman
Bugaje, wanda ya ki karbar tayin mukamin. 

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Majalisa ta yi watsi da sunayen jakadan da Buhari ya aika"

Post a Comment