A Kenya wasu iyaye sun raɗa wa ɗansu suna Donald Trump

Wasu iyaye sun bayyana dalilin da ya sa suka
sanya wa jaririnsu sunan sabon zababben
Shugaban Amurka Donald Trump, bayan da ake
ta sukansu kan yin hakan.
An haifi jaririn wanda cikakken sunansa shi ne
Donald Trump Otieno, ranar tara ga watan
Agusta a yankin Kisumu na yammacin ƙasar.
Kuma iyayen nasa sun yanke shawarar raɗa
masa wannan suna ne mai jawo ce-ce-ku-ce,
saboda sun yaba da aƙida da manufar Mista
Trump, kamar yadda jaridar Daily Nation ta
Kenyan ta ruwaito.
Mahaifin jaririn mai suna Felix Otieno, ya ce sun
sanya wa ɗan nasu sunan ne tun kafin
hamshakin ɗan kasuwar ya kayar da Hillary
Clinton a zaɓen shugaban Amurkan.
Mista Otieno ya bayyana cewa, '' a lokacin ba ni
da tabbacin Trump zai bayar da mamakin da ya
bayar na nasarar da ya yi, amma dai ina da
yaƙinin cewa yana da cancanta ta zama
shugaba.''

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "A Kenya wasu iyaye sun raɗa wa ɗansu suna Donald Trump"

Post a Comment