Keane na Hull zai yi jinyar shekara daya

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Hull City,
Will Keane, zai yi jinyar shekara daya,
sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa.
Keane mai shekara 23, ya yi rauni ne a karawar
da kungiyarsa ta ci Southampton a ranar 6 ga
watan Nuwamba.
Dan kwallon ya koma Hull City da murza-leda
daga Manchester United a ranar 30 ga watan
Agusta, kuma tuni ya yi wasanni shida a
kungiyar.
Keane ya taba yin doguwar jinya a shekarar 2012
a rauni iri daya da wanda ya yi a yanzu a lokacin
da yake taka-leda a matasan tawagar kwallon
kafa ta Ingila masu shekara 19.
Hull City tana mataki na 18 a kan teburin
Premier.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Keane na Hull zai yi jinyar shekara daya"

Post a Comment