An dage karawa tsakanin Madrid da Valencia

Hukumar kwallon kafa ta Spaniya ta dage wasan
cin kofin La Liga tsakanin Real Madrid da
Valencia wanda aka tsara za su kara a ranar 18
ga watan Disamba.
An dage karawar ne saboda da Madrid za ta
buga wasan gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da
za a yi a cikin watan Disamba, inda za ta wakilci
nahiyar Turai, bayan da ta ci kofin zakaru na 11
na Turai a tarihi.
Tun farko an tsara cewar Real Madrid za ta
ziyarci Valencia a wasannin mako na 16 a gasar
cin kofin La Liga a ranar Lahadi 18 ga watan
Disamba, amma an dage wasan zuwa wani
lokaci.
Madrid wadda ta lashe kofin duniya na zakarun
nahiyoyi a shekarar 2014, tana mataki na daya a
kan teburin La Liga da maki 27, yayin da
Valencia ke matsayi na 15 da maki 10.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An dage karawa tsakanin Madrid da Valencia"

Post a Comment