Marcelo ya cika shekara goma a Real Madrid

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Brazil,
Marcelo Vieira, ya cika shekara goma yana taka
leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Madrid ta gabatar da Marcelo a gaban 'yan jarida
a ranar 15 ga watan Nuwambar 2006, a lokacin
yana da shekara 18.
Dan wasan mai tsaron baya, ya buga wa Real
Madrid wasanni 372, ya kuma ci mata kwallaye
26 tun komawarsa can da taka-leda.
Marcelo ya lashe kofuna 12 a Real Madrid ciki
har da kofin zakarun Turai biyu da kofin duniya
daya na zakarun nahiyoyi da UEFA Super Cup
biyu da na La Liga uku da Copa del Rey biyu da
kuma Spanish Super Cup biyu.
Dan kwallon shi ne ke matsayi na biyu a matakin
dan wasan waje da ya buga wa kungiyar
wasanni da yawa, bayan Roberto Carlos wanda
ya yi wasanni 527.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Marcelo ya cika shekara goma a Real Madrid"

Post a Comment