India: Sabbin takardun kudi sun fara karanci

Jama'a sun sake yin jerin gwano a kofar
bankunan kasar India, saboda kokarin sauya
tsaffin takardun kudin kasar da sabbin bugawa.
Wakilin BBC a birnin Kolkata ya ce yawancin
shaguna a birnin ba su yi ciniki ba saboda
abokan huldarsu ba su da kudade a hannu.
Wakilin ya kara da cewa an bi tsari a dogon layin
da ke bankuna a jiya alhamis, amma daga bisani
sai mutane suka fusata saboda bankunan sun
fara sanar da cewa sabbin takardun kudin na gab
da karewa.
Firaiminista Narendra Modi dai bai wani sanar da
batun sauyin kudin ba ga al'umar kasar, kwatsam
sauyin ya faru a cikin makon nan a kokarin
gwamnatinsa na ceto darajar kudin kasar Rufi
daga sake durkushewa.
Harwayau a kasar ta India wata gobara ta tashi
a kamfanin saka tufafi da ke wajen babban birnin
kasar Delhi.
Mutane sha uku ne suka rasu a gobarar, kuma
mai magana da yawun 'yan sandan birnin ya ce
wadanda lamarin ya rutsa da su ma'aikatan
kamfanin ne da suke kwana a wurin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "India: Sabbin takardun kudi sun fara karanci"

Post a Comment