Nigeria: Buhari ya rantsar da sabon alkalin alkalai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya
rantsar da Walter Onnoghen a matsayin alkalin
alkalan kasar na riko.
Mista Onnoghen ya maye gurbin mai shari'a
Mahmud Mohammed wanda ya yi ritaya a ranar
Laraba.
An yi bikin rantsuwar ne a fadar shugaban kasar
da ke Abuja.
Mai shari'a Walter Onnoghen ya karbi wannan
mukami ne a daidai lokacin da fannin shari'ar
kasar ke cikin mawuyacin hali saboda zargin cin
hanci da rashawa.
A watan da ya gabata ne jami'an tsaro suka
kame wasu manyan alkalai bakwai a wani
bangare na binciken da ake yi.
Hukumomi sun ce sun gano dubban daloli a
gidajen alkalan, wadanda aka bayar da belinsu,
amma har yanzu ba a tuhume su a kotu ba.
Batun dai ya raba kan lauyoyi da sauran masu
ruwa da tsaki a fagen shari'ar kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Buhari ya rantsar da sabon alkalin alkalai"

Post a Comment