Mourinho zai yi tankade da rairaya a United

Kocin Manchester United Jose Mourinho yana
yin bincike kan dukkan al'amuran da suka shafi
kungiyar, yana mai cewa ya yi mamakin yadda
ya gaji wasu abubuwa a kungiyar.
Rahotanni na cewa Mourinho bai ji dadin yadda
ake tafiyar da sashen kula da lafiya na kungiyar
ba.
An fahimci cewa bayan da ya karbi United daga
hannun Louis van Gaal, Mourinho ya kula cewa
tsare-tsaren kungiyar a fannoni da dama ba su
kai yadda yake so ba.
Mourinho ya lashe kofuna 23 a lokacin da yake
Porto da Chelsea da Inter Milan da kuma Real
Madrid.
Ya fito fili ya tuhumi 'yan wasa Luke Shaw da
Chris Smalling saboda rashin buga wasan da
suka doke Swansea da ci 3-1 ranar Lahadi
saboda raunin da suka ji, inda ya shaida wa
manema labarai cewa: "Ya kamata mu inganta
wannan kungiyar ta kowanne fanni."
BBC Sport ta fahimci cewa Mourinho, mai
shekara 53, yana son yin garanbawul a kowanne
bangare, ciki har da fannin zirga-zirga da zuwa
wasannin sada zumunci da motsa jiki da kimiyyar
wasanni da tsarin zuba 'yan wasa.
A farkon kakar wasa ta bana, tsohon kocin na
Chelsea ya yi hasashen cewa United za ta yi
gogayya wajen cin kofin Premier.
Sai dai galabar da suka yi a kan Swansea, wacce
ke ta biyun karshe a tebirin Premier, ita ce
nasara ta biyu da suka yi a wasanni takwas da
suka yi a Premier.
Yanzu dai su ne a matsayi na shida a gasar -
inda suke bayan ja Liverpool, wacce take ta
daya, da maki takwas.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mourinho zai yi tankade da rairaya a United"

Post a Comment