Nigeria: An yi watsi da kasafin kudin hukumar tara haraji ta FIRS

Majalisar dattijai ta Nigeria ta yi watsi da
kasafin kudin da hukumar tara kudin shiga ta
kasar (FIRS) ta gabatar mata.
Majalisar tace ta yi hakanne saboda hukumar
bata fayyace mata dalla-dalla abubbuwan da
zata yi da kudaden da ta sa a kasafin kudin da
ta gabbatar mata na wannan shekarar ba.
A ranar Alhamis ne dai 'yan majalisar suka yi
watsi da kasafin kudin na hukumar tara kudi ta
kasa
Hakan ya biyo bayan shugaban majalisar Bukola
Saraki ya amince da shawarar da kwamitin kudin
majalisar ya bayar.
Kwamitin ya ce hukumar tara kudi ta kasa bata
zauna ta yi cikakken nazari ba kafin ta shirya
kasafin kudin ta na wannan shekara.
Abinda yasa ta kasa bada cikakken bayanai kan
irin manyan ayyukan da take son ta aiwatar,
wanda kuma yasa hukumar tayi ta maimaita
wasu ayyukan a kasafin kudin.
A wani jawabi da ya gabatar, Bukola Saraki yace
a matsayin su na masu sa ido, "dole ne majalisar
ta tabbata ta tattance duk ayyukkan da za'a
aiwatar a kasar ta kuma tabbatar da cewa an
kashe dai-dai kudin da ake bukata kan ko wanne
aiki ba tare da anyi kari ba.
Bayan jawabin nasa ne dai 'yan majalisar sukayi
watsi da kasafin kudin da murya daya.
'Yan Najeriya da dama na zargin cushe a kasafin
kudin kasar na 2016.
Hakan ne dai yasa shugabannin majalisar
dattijan kasar sukayi wa 'yan kasar alkawarin
tabbatar ba a yi wani cushe ba a kasafin kudin
kasa ko na wata ma'aikata.
Masana na ganin wannan matakin da 'yan
majalisar suka dauka zai iya kawo tsaiko wajen
aiwatar da aiyukkan hukumar ganin cewa ta
gabatar da kasafin kudin a makare.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: An yi watsi da kasafin kudin hukumar tara haraji ta FIRS"

Post a Comment