An kai hari ofishin jakadancin Jamus a Afghanistan

Wani bam da aka dasa a cikin mota ya tashi a
ofishin jakadancin kasar Jamus da ke arewacin
birnin Mazari sharif a Afghanistan, ya kuma
hallaka mutane biyu.
Wani jami'in lafiya a asibitin yankin ya shaidawa
BBC cewa an kawo fiye da fararen hula tamanin
da suka jikkata asibiti, yawancin su kuma gilasan
da suka farfashe ne suka ji musu raunin.
Mai magana da yawun kungiyar tsaro ta NATO a
birnin ya ce an shiga da motar da aka makareta
da bama-bama cikin ginin ofishin, lamarin da ya
janyo mummunar barna.
Jim kadan da tashin bama-baman kuma sai aka
fara harbe-harben kan mai tsautsayi, kuma tuni
kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.
Ko a baya ma 'yan kungiyar Taliban sun sha kai
hare-hare irin wannan a birnin na Mazari Sharif,
wanda shi ne birni na uku mafi girma a kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kai hari ofishin jakadancin Jamus a Afghanistan"

Post a Comment