Dan wasan kokawar Gambia ya nutse a teku

Kocin shahararren matashinan dan wasan
kokawa na kasar Gambia ya ce dan wasan ya
nutse lokacin da ya yi kokarin ketarawa zuwa
turai daga tekun Bahar rum.
Ali Mbengu, mai shekara 22, ya gamu da ajalinsa
ne lokacin da jirgin ruwan yake ciki ya kife yayin
da suke hanyarsu ta zuwa Italiya daga Libya.
Wasan kokawa na da magoya baya sosai a
Gambia da kuma makwabciyarta Senegal kuma
hukumar kokawa ta kasar ta yaba wa marigayin
a kan kwazon da ya nuna a wasan.
A farkon watan da muke ciki mai tsaron ragar
kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar ta rasu
lokacin da ta yi kokarin ketara tekun bahar rum
domin zuwa turai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dan wasan kokawar Gambia ya nutse a teku"

Post a Comment