Dan bindiga ya kashe masu kallon kwallo 13

Wani dan bindiga a kasar Sudan ta kudu ya
kashe kimanin mutane 13 dake kallon
kwallon gasar firmiya da aka fafata tsakanin
Chelsea da Everton a karshen makon daya
gabata.
Jaridar Yahoo Sport ta ruwaito mataimakin
Kaakakin hukumar yansanda Kwacijwok
Dominic Amondoc yace yawan mutanen da
suka rasa rayukansu yayin harbin sun haura
zuwa 13 sakamakon wasu da suka jikkata a
harin suma sun mutu.
Amondoc yace akwai sauran mutane 10
dake samun kulawa a asibiti. Wani daga
cikin wadanda suka ji raunuka daga harbin
Wani Patrick yace “lokacin da ya harbe ni,
sai na fadi kasa warwas, amma sai wasu
matasa ma suka fado kai na, haka na kasa
dagowa har sai da ya karar da harsashinsa,
jama’a da dama sun mutu”
Ana tsammanin dan bindigan a buge yake,
wato sai da ya sha giya yayi tatil. Da fari ya
nuna bacin ransa kan an hana shi shiga
gidan kallon kwallon, saboda yace sai dai ya
shiga kyauta ba zai biya kudi ba, alhali kudin
shiga gidan kallon $0.50, kwatankwacin
N230.
Da yaga ba za’a kyale shi ya shiga bane, sai
ya koma gida ya dauko bindiga ya dinga
harbin mai kan uwa da wabi” inji Amondoc.
Sai dai zuwa yanzu ba’a san inda dan
bindigan ya shige ba, amma an fara gudanar
da bincike, inji Mataimakin Kaakakin
gwamati Paul Akol Kordit.
A wasan da lamarin ya faru Chelsea tayi
lagalaga da Everton da ci 5-0 a filin wasa na
Stamford Bridge mallakan Chelsea, inda
Eden Hazard yaci kwallaye 2, sai Diego
Costa, Marcos Alonso da Pedro Rodriguez
suka zura daya daya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dan bindiga ya kashe masu kallon kwallo 13"

Post a Comment