Brazil ta lallasa Argentina da ci 3-0

Neymar da Philippe Coutinho kowannen su ya
zura kwallo guda a wasan da Brazil ta doke
Argentina da ci 3-0 a wasan neman cancantar
shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.
'Yan wasan Argentina, cikin su har da Lionel
Messi sun yi kokarin yin tasiri a wasan, sai dai
Paulinho ya zura tasa kwallon.
Yanzu dai Argentina tana mataki na shida a cikin
tawaga 10 daga yammacin Amurka da ke son
shiga gasar cin kofin duniya, kuma tuni hudu
daga cikin su suka cancanci shiga gasar.
Argentina tana da makin 16 a wasa 11 da ta
buga, wato tana bayan Ecuador, wacce take ta
hudu da maki daya, kuma ita ce ta takwas a
bayan Brazil, wacce ke da maki 24

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Brazil ta lallasa Argentina da ci 3-0"

Post a Comment