Real Madrid ta yi wasa 28 ba a doke ta ba

Real Madrid ta yi wasa 28 a jere ba tare da an
doke ta ba a dukkan fafatawar da ta yi tun daga
kakar bara zuwa bana.
Madrid - karkashin jagorancin Zinedine Zidane -
ta fara da doke Eibar 4-0 a ranar 9 ga watan
Afirilun 2016, daga nan ta ci wasa 9 jumulla daga
11 da ta yi, daga nan ta lashe kofin zakarun
Turai na 11 a Milan.
Real Madrid ta fara da lashe UEFA Super Cup a
kakar bana, kuma a kakar shekarar nan ta yi
wasa 17 ta lashe guda 12 ta yi canjaras a
fafatawa biyar, sannan tana mataki na daya a
kan teburin La Liga.
Jumulla Madrid ta yi wata takwas ba ci ta a
wasa ba a jere ta samu nasara a karawa 21 da
kuma yi canjaras a wasa bakwai.
Hakan na nufin kungiyar ta yi gumurzu sau 18 a
gasar La Ligar Spaniya, sannan ta yi guda
takwas a gasar cin kofin Zakarun Turai, ta kuma
buga sauran wasannin a Copa del Rey da UEFA
Super Cup.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Real Madrid ta yi wasa 28 ba a doke ta ba"

Post a Comment