Za mu iya kai wa gasar kofin duniya — Bale

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Wales,
Gareth Bale, ya ce suna da kwarin gwiwar cewar
za su samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya
duk da kunnan doki 1-1 da suka tashi da Serbia
a ranar Asabar.
Kasashen biyu sun fafata ne a wasan shiga
gasar cin kofin duniya, inda Bale ya fara ci wa
Wales kwallo daga baya Aleksandar Mitrovic ya
farke ta da ka.
Da wannan sakamakon Wales tana mataki na uku
a kan teburin rukuni na hudu, inda Jamhuriyar
Ireland wadda ke mataki ta ba ta tazarar maki
hudu, za kuma su fafata a tsakaninsu a Dublin a
ranar 24 ga watan Maris.
Wasan da Wales ta yi a ranar Asabar a filinta da
ke Cardiff shi ne na uku da tawagar ta yi
canjaras a fafatawa uku a jere, kuma ita ce ke
fara cin kwallo daga baya a farke.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Za mu iya kai wa gasar kofin duniya — Bale"

Post a Comment