Biritaniya: Yarima Harry ya ce Meghan ce budurwarsa

Yarima Harry ya tabbatar wa duniya cewa
Meghan Markle budurwar sa ce.
Yariman ya fitar da wannan sanarwar ne a
hukumance daga fadar Kensington, inda ya soki
kafofin yada labarai kan yadda suka yi ta
tsangwamar budurwar tasa.
Sanarwar ta ce masoyan biyu, sun yi watanni
hudu da fara soyayyar tasu, kuma bai kamata a
sanya Misis Markle a gaba da zage-zage ba.
Yariman ya kara da cewa, shi bai cika daukan
mataki a hukumanci kan rade-radin da basu da
tushe ba, amma a cewarsa, wannan karon ture
ya kai bango.
A 'yan kwanakin da suka wuce, jaridun kasar sun
yi ta yada labarai kan Misis Markle mai shekaru
35, wacce aka fi sani da Rachel Zane, saboda
fitwar ta a wani shirin talabijan mai suna 'suits'.
Dangantakar Yarima Harry da manema labarai ya
dade da yin tsami dai, tunda ya dade yana yi
masu kallon suna yi wa masarautarsu shisshigi
dayawa, har dai yadda suka shiga rayuwar
mahaifiyarsa, marigayiya Diana, Gimbiyar Wales.
A lokacin da ya ke da shekaru 20 kuma, an dauki
hoton sa yana fada da masu daukan hoto a wani
wajen shakatawa a London.
A shekarar 2012 kuma an fitar da wasu hotunan
sa tumbur babu kaya, a wani otal da ke Las
Vegas a Amurka.
Amma kuma Yarima Harry ya fice matuka wajen
ayyukan sa na bayar da agaji, da kuma
jaruntakarsa a ayyukan soja.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Biritaniya: Yarima Harry ya ce Meghan ce budurwarsa"

Post a Comment